Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta cafke wani magidanci mai suna Hassan Azeez, mai shekara 46 a duniya bisa zargin kwarawa matar sa man fetur sannan ya cinna mata wuta.
Kakakin rundunar ƴan sanda jihar, SP Abimbola Oyeyemi itace ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar. Rahoton shafin Linda Ikeji ya tabbatar.
KU KARANTA KUMA: Abun tausayi: Bidiyon attajirin da ya samu lallurar taɓin hankali ya sosa zuciya
A cewar ta an cafke wanda ake zargin ne bayan an shigar da ƙorafi a ofishin ƴan sanda na Ibogun, wanda mahaifiyar matar ya shigar cewa a ranar 22 ga watan Oktoban 2022, mijin ƴar sa mai suna Olayinka Hassan, ya cinna mata wuta bayan sun ɗan samu saɓani a tsakanin su. Inda daga nan aka wuce da ita zuwa wani asibiti a birnin Ibadan.
“Bayan samun ƙorafin, DPO na Ibogun, CSP Samuel Oladele ya tura jami’an ƴan sanda cikin gaggawa zuwa gidan. Amma kafin su ƙarasa gidan wanda ake zargin ya ranta a na kare. Tun daga wannan ranar ƴan sanda suka bazama nemanss har zuwa ranar 22 ga watan Janairun 2023, lokacin da aka samu nasarar cafke shi.”
“A yayin da ake tuhumar sa, wanda ake zargin ya amsa laifin sa inda yace ya tsere ne zuwa ƙasar Benin, sannan ya ɗora alhakin hakan akan shaiɗan.”
“A cewar sa, yace matar sa ta dafa masa abinci, amma a maimakon hakan sai ta cigaba da yin wankin kaya kawai abinta. Ya kuma ƙara da cewa ya fusata saboda yana matuƙar jin yunwa wanda fusatar ce ta sanya ya kwarara mata man fetur ya cinna mata wuta.”
“Da aka tambaye shi ko kayan waye take wankewa, sai ya kada baki yace kayan sa ne.” A cewar Oyeyemi.
Tuni aka tura wanda ake zargin zuwa sashin laifukan kisan kai na hukumar domin cigaba da gudanar da bincike.
An Kuma: Wani Mutum Ya Faɗi Matacce a Layin Cirar Kuɗi a Banki
A wani labarin na daban kuma, wani magidanci ya mutu akan layin cirar kuɗi a banki.
Wani abun ban takaici ya sake aukuwa inda wani mutum ya faɗi ya mutu a cikin banki a yayin da yake ƙoƙarin ciro kuɗi.