Wata mai gidan abinci ta wulakanta wani kwastomanta a lokacin da yayi hunkurin biyanta kuɗin abincin da yaci da sabuwar takardar kuɗi na Naira ta 1000 wacce babban bankin kasar nan na CBN ya buga.
Mutumin ya shiga gidan abincin ne sannan kuma ya cika cikinsa da abinci, yayin da yake kokarin biyan matar mai gidan abinci da kudin abincin da yaci da sabuwar Naira1000, ta ce sam ita bata san da wannan kuɗin ba.
A bidiyon da ya bazu a shafin sada zumunta na Twitter a ranar Juma’a, matar ta cakume shi sannan kuma ta hana shi tafiya har sai da ta yaga masa wando ta kusa yi masa tsirara a bainar jama’a.
A faifan bidiyon, wata mata ta yi kokarin fadakar da mai gidan abincin cewa sabon kuɗi ne amma matar ta ƙi.
Ta cigaba da cewa lallai sai ya biyata da tsohon kudin da ta sani ba wannan ba.
Ta ce: “Ka biyani kuɗi na, wannan wani irin rainin hankali ne .” “Ni ban taɓa ganin irin wannan kuɗin ba, kuma dan haka ba zan karɓa ba.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Mata Ta Haihu Lokaci Kaɗan Bayan Likita Yace Ɗan Dake Cikinta Bashi Da Rai
Shi kuma mutumin yace: “Wannan sabon kuɗi ne na Naira.”
Cikin ƙanƙanin lokaci matar ta tara masa jama’a kuma ta fara yunkurin kiransa da barawo.
Wannan na nuni karara cewa babban bankin CBN bai wayar da kan jama’a yadda ya kamata ne gashi saura wata guda da a daina amfani da tsohon Naira.
Kalli faifain bidiyon a NAN
Yayin da aka tuntuɓi kakakin babban bankin kasar nan CBN, Osita Nwanisobi, ya bayyanawa majiyarmu cewa babban bankin na CBN yana iyakacin kokarinsa wajen ganin ya wayar da kan yan Najeriya kan sabbin takardun Naira.
Ya kara da cewa zasu haɗa kai da hukumar wayar da kai ta kasa NOA domin zurfafa wayar da kan jama’a musamman waɗan da ke karkara da basu da labarin halin da ake ciki a birni.
Ya kara da cewa: “Muna kokarin cigaba da wayar da kan mutane, kuma muna hada kai da hukumar wayar da kai saboda kowa ya samu labari, har da karkara.”