By Abbas Yakubu Yaura
Wasu mahara da har yanzu ba a tantance ko su waye ba sun kashe wani uba tare da ‘ya’yansa maza biyu a ranar Alhamis a hanyarsu ta dawowa daga gona a unguwar Ore kusa da titin Ore Egbeba na gundumar Apa-Agila dake karamar hukumar Ado ta jihar Benue.
Wakilinmu ya rawaito cewa an yi ta samun kashe-kashe a wasu yankunan Ado dake kan iyaka da jihar Ebonyi inda rikicin kan iyaka ya ci gaba da dagula al’ummar mazauna yankin yayin da kuma aka samu rahoton harin da makiyaya suka kai.
Mazauna yankin sun ce kisan na baya-bayan nan na ‘yan uwa uku wanda aka bayyana sunayensu da Mista Enogu, da Chigbo Enogu da kuma Sunday Enogu, kisan kai ne daya yi yawa, saboda mutanen yankin ba sa iya motsawa cikin walwala don yin abubuwan da suka dace.
Mazauna kauyen sun ce wadanda suka mutun sun je gonar su ne lokacin da aka kai musu harin tare da kashe su yayin da suke komawa gida bayan kammala aikin wannan ranar.
Shugaban karamar hukumar Ado, James Oche, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Makurdi, inda yace ya samu labarin kashe ‘yan uwa uku cikin kaduwa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Oche yace, ba tare da bata lokaci ba an kai rahoton lamarin ga hukumomin tsaro wadanda tuni jami’an su na kan bin diddigin wadanda suka aikata wannan aika-aika duk da cewa an kama wasu ‘yan kadan kuma wadanda ake zargin zasu taimaka wajen gudanar da cikakken bincike.
Kazalika Shugaban ya kuma bukaci al’ummar yankin dasu ci gaba da zaman lafiya da bin doka da oda domin ya tabbatar musu da cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Ado.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benue, DSP Catherine Anene, ita ma ta tabbatar da faruwar lamarin.