By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Adavi da ke jihar Kogi, inda suka kashe ‘yan sanda uku.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi (PPRO), SP William Ovye Aya, ne ya bayyana hakan a Lokoja ranar Asabar a wata sanarwa daya fitar.
Da Dumi-duminsa: Sarkin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi Ya Rasu Yana Da Shekaru 83
Ya ci gaba da cewa, “A yau 23/4/2022 rundunar ‘yan sandan ta samu rahoton afkuwar lamarin da ya faru a ofishin ‘yan sanda na Adavi, inda wasu ‘yan iska suka far wa ofishin daga wani bangare suna harbe-harbe ba da dadewa ba, amma jami’an da ke bakin aiki da jami’an tsaro na sashin mayar da martanin gaggawa suka fatattake su wadanda suke gudanar da ayyuka na musamman a karamar hukumar.”
Ya kara da cewa, “Rundunar ta rasa jami’anta uku a yayin fafatawar, yayin da ‘yan bindigar suka gudu da raunukan harbin bindiga saboda sun kasa samun damar shiga ofishin.”
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Edward Egbuka, ya tura tawagar ‘yan sanda zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya tare da zakulo barayin.
Ya kara da cewa, “Don haka rundunar ‘yan sandan jihar ta yi kira ga al’ummar Adavi da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da su da su sanya ido tare da kai rahoton duk wani ko gawar da aka gani da raunukan harsashi, ga ‘yan sanda ko kuma jami’an tsaro da ke kusa da su.
“A halin da ake ciki, CP Egbuka ya umarci mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, da ya fara gudanar da bincike kan lamarin nan take.”
Comments 1