Wani kwararowar iskar sinadarin chlorine mai guba a tashar ruwa ta Aqaba dake Jordan ta kashe mutane 11 tare da jikkata wasu fiye da 250.
Kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito, Hukumomin kasar sun ce wani kwandon sinadari ne ya fado a lokacin da ake jigilar su.
Hotunan na’urar CCTV suna nuna an daga kwantenan cikin iska sannan ba zato ba tsammani ta fado kan jirgin ruwa ta fashe.
An hangi yadda wajen ya turnuƙe da hayakin iskar gas din mai haske inda yake bazuwa a kasa, lamarin da ya sanya mutane gudu don tsira.
Kafofin yada labarai na kasar sun ce 199 daga cikin wadanda suka jikkata na samun kulawa a asibitocin yankin saboda kamuwa da sinadarin.
Rahotanni sun ce wasu na cikin mawuyacin hali, a don haka aka shawarci mazauna birnin Aqaba mai tazarar kilomita 16 daga arewa da tashar jiragen ruwa da su kasance a ciki tare da rufe tagogi da kofofi biyo bayan ruwan.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, an kwashe gabar tekun kudancin Aqaba mai nisan kilomita 7 kacal, kuma sanannen wurin yawon bude ido ne kuma Ma’aikatar Tsaron farar hula ta aike da tawagar kwararru zuwa tashar jiragen ruwa domin shawo kan lamarin.