Wasu bayanai da aka samu a kotu kolin Amurka na nuni da cewa A kwai yiyuwar Babbar kotun kasar ta soke wata dokar da aka amince da ita a fadin Amurka da ta bayar da damar zubar da ciki.
Rayhaan Radiyo ta tabbatar da cewa matakin ya haifar da masu goyon bayan lamari da masu adawa da shi sun gudanar da zanga zanga a wajen harabar kotun a jiya litinin.
A shafi na 98 na bayanan farkon akan hukunci mai shari’a Samuel Alito ya bayyana cewa amincewa da dokar zubar da ciki da Roe v Wade yayi tun a shekarar 1973 a fadin kasar babban kuskure ne.
Kafar yada labarai ta News outlet, ta ambato mai shari’a Alito yana cewa matakin yana da illoli sosai.
Idan dai babbar kotun ta Amurka ta soke hukuncin , sabuwar dokar zata haramta zubda ciki a jihohi 22 na kasar Amurka.
Sai dai sai a watan Juli ne ake sa ran yanke hukuncin karshe kan wannan batun Mai cike da cecekuce.
Amma an ambato, shugabar majalisar kasar Nancy Pelosi da shugaban masu rinjaye Chuck Schumer wadanda dukansu yan jamiyar Democract ne suna cewa , idan dai rahoton ya tabbata, Babbar kotun na kokarin dakile yancin dan adam wanda ba ataba yin irin hakan ba a cikin shekaru 50 da suka gabata
Har kawo yanzu Babbar Kotun da Fadar white house ba suce ufam ba akan lamarin.
A wani labarin Kuma na daban.
Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne an banka musu wuta inda suka kone kurmus a garin Kanshio da ke wajen garin Makurdi a jihar Benue.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa, an bi su ne da sanyin safiyar ranar Litinin, inda aka kama su daura da makarantar Divine Mercy Minor Seminary da ke Kanshio inda a karshe aka kona su.
An tattaro cewa wadanda ake zargin wadanda tun farko su uku ne amma daya daga cikinsu ya tsere a lokacin da ake binsa, sun samu shiga wani gida da karfi da yaji a garin Kanshio a kokarinsu na yi wa dangi fashi bayan sun yi harbin gaggawa don kaucewa shiga tsakani.
Sai dai kuma sa’a ya ci karo da su, inda aka ce shugaban gidan ya yi ta maza inda ya kama daya daga cikinsu, lamarin da ya sa sauran mutanen biyu suka shiga tsakani da wannan jarumin har suka kubutar da abokin aikin nasu.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa wadanda ake zargin bayan ceto dan kungiyar nasu ne suka gudu ta hanyar tsallaka katanga inda suka hau kan babur da ke jiran su a bakin titi amma wadanda abin ya shafa suka nemin taimakon mazauna yankin lamarin da ya jawo hankalin wasu matasa da ke yankin.
Matasan dai kamar yadda aka samu sun fatattaki wadanda ake zargin har ta kai da biyu daga cikinsu suka makale a kusa da makarantar Seminary inda nan take suka banka musu wuta yayin da sauran suka tsallake rijiya da baya ta katangar makarantar suka tsere.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Benue PPRO, SP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin.
“An tabbatar da al’amura. Ana ci gaba da bincike, don Allah, ”in ji Anene a cikin wani sakon rubutu.