Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya bayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda na karshe da ya kamata a kawar da su.
Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da babban hafsan sojin kasa, Janar Faruk Yahya, ya kai masa ziyarar Sallah a ranar Talata.
“Ba za mu taba barin ’yan ta’adda su samu yadda suke so ba. Dabarun ya kamata muyi amfani da su don mu kayar da su shi ne mafi alheri a gare mu baki daya.”
Sarkin Musulmi ya ce kalubalen da ake fuskanta shi ne gwada karfin jami’an tsaro.
Ya ci gaba da cewa “Kamar ranar da shugaban kasa ya yi a ranar Sallah, ni ma na yi imanin cewa za mu kawo karshen su.”
Sai dai babban hafsan sojin ya yi alkawarin binciko Bello Turji da sauran ‘yan bindiga da ke addabar yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da ginin sansanin soji domin yakar ‘yan ta’adda a karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto ranar Talata, ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda bazasu Sami sakat ba a kasar nan.
“Za mu isa inda suke boye, mu fatattake su, mu kwaso makamansu,” in ji shi
“Mun san yadda Isa yake da mahimmanci ga aikinmu. Yana da matsayi mai mahimmanci a cikin aikinmu. Muna kafa sansani na gaba a muhimman wurare a kokarinmu na inganta kai wa ga ‘yan fashi, ‘yan ta’adda da sauran masu laifi hari, mu fatattake su da kuma kwato makamansu,” inji shi.
Ya ce, za a tura karin dakaru, kayan aiki da sauran masu taimaka wa Sojojin da aka jibge a sansanin.
Ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa goyon bayan da yake baiwa rundunar soji.
A wani labari Kuma na daban.
Bulletin: World Press freedom day
Hadadiyar gungiyar kwararuru masu aikin tace labaru ta kasa (NGE) tace hakkinan na nema tare da watsa labarai ba tare da wata turjiya ba na cikin wani hali a Nijeriya .
Shugaban Kungiyar na kasa , Mustapha Isah , da babban sakataren Kungiyar , Iyobosa Uwugiaren ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwa da suka fitar a yau yayin bikin ranar yancin yan jaridu ta duniya.
Saboda haka, sunyi kiran gaggawa domin kare kafafen yada labarai daga koma baya, inda suka bayyana cewa Dimokuradiyya zata samu koma bayane idan ana yima yancin yada labarai barazana.
Kungiyar ta NGE tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta sauwaka farashin kayyakin da kafafen yada labarai da gidagen jaridu ke amfani dasu ,kana a saukaka haraji ga kafafen yada labarai, domin ceto su daga durkushewa.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta ayyana 3 ga watan mayun ko wace shekara a mastayin ranar bikin yancin yan jaridu, domin fadakar da al’umma akan muhimanci baiwa kafafen yada labarai da yan jaridu yancinsu, kuma a tunatar da gwamnatoci bukatar da ke akwai na martaba yancin fadin alabarkaci baki kamar yadda sashe na 19 na kundin tsarin majalisar Dinkin duniya ya amince dashi tun a shekarar 1948.
Ranar dai ta kasaence ranar da kwararurun yan jaridu ke tattunawa akan Yancin aikin jarida da kuma ka’idojin aikin.
Taken bikin na bana shine “Aikin jarida a zamanan ce” inda ake amfani da abuwa da dama na zamani domin binciko muradun al’uma.
Comments 1