Kungiyar matasa mai zaman kanta na ‘Noble Youth Mass Support Association (NYMSA),’ ta shawarci gwamnati a dukkanin matakai da su rika sanya matasa a cikin gudanar da harkokin mulkinsu domin ci gaban dimokuradiyya.
Godwin Onmonya, shugaban kungiyar na kasa, shi ne ya bayyana hakan a yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja a lokacin bukin ranar dimokuradiyya.
Shugaba Buhari ne dai ya ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokuradiyya.
A cewar kungiyar, lokaci ya yi da gwamnatoci za su rika sanya matas a cikin harkokin gudanar da mulki domin cimma manufofin SDGs wanda zai taimaka wajen dakile kalubalen da ake fuskanta a duniya.
Daga cikin manufofin SDGs din akwai kawo gyara ta fuskacin tattalin arziki da kuma zamantakewa tare da kawo ci gaba a sha’anin gudanar da rayuwa.