Ana zargin Wata Malamar makarantar Kwalejin tarayya dake Kwali na yankin Kuje dake Babban Birnin Tarayya Abuja, da dukan wani dalibin ta Mai suna Yahaya Aliyu har lahira.
Malamar Mai suna Mrs Gibson an ruwaito cewa, ta daki dalibin ne Mai shekara 13, dake aji 2 a makarantar Sakandare, sabida ya ki yin aikin gida wato Assignment.
Wani shaidan da ya bukaci jaridar Dimokuradiyya ta sakaye sunan shi ya ce, Aliyu bai sami kammala aikin gidan ba ne, sabida ba ya jin dadi, Wanda kuma ya ziyarci dakin shan magani dake Makarantar, kafin afkuwar lamarin.
Shaidan ya bayyana cewa, “A ranar Litinin 9 ga watan Ogustan shekarar nan, Aliyu bai da lafiya, wanda kuma har yasa ya ziyarci dakin shan maganin makarantar, Amma ba’a ai mai allurai ba, sabida bai ci abinci ba a ranar” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gobarar Tankar Mai: Mutum 2 Sun Mutu, Motoci 14 sun kone, a Anambra
” Hakan ya sa Aliyu ya dawo aji, ya yin da takwarorin shi dalibai ke bada aikin gidan, sai kuma Malamar ta tambaye shi Ina na shi, Amma Aliyu bai kammala ba” a cewar shi.
“Hakan yasa, Malamar ta fara bashi gwale-gwale, daga bisani kuma ta fara dukar shi da hannun bokiti akai, anjima kadan sai ya sanya kanshi akan teburi” inji shaidan
Shaidan ya ci gaba da cewa, ” ko da sauran daliban su ka lura cewa, Aliyu ya kwanta shiru, sai suka duba shi, daga nan kuma su ka yi hanzarin kai shi asibiti, inda a can ne ya mutu” kamar yadda ya bayyana.
Majiyar Dimokuradiyya ta kuma ruwaito cewa, bayan rasuwar Aliyu, Daliban Makarantar sun fara zanga-zanga a cikin harabar makarantar.
Ko da aka tuntumi jami’ar hulda da jama’a na rundunar yan sandan garin Abuja Mariam Yusuf, ta tabbatar da afkuwar lamarin , inda kuma ta ce, Yan sanda na gudanar da bincike kan lamarin.