Wata mata ƴar shekara 43 a duniya ta shiga hannun hukuma bisa zargin lakaɗawa mijinta dukan tsiya da ƙona gidan da suke zaune a ciki.
Matar mai suna Florence Karakacha ta shiga hannu ne a ranar Asabar, 28 ga watan Janairun 2023, a yankin Navakholio, Kakamega na ƙasar Kenya. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: APC ta nemi IGP ya hukunta ɗan takarar gwamnan PDP bisa zargin sa cin zarafin DPO
Shugaban jami’an ƴan sanda na Navakholio, Richard Omanga ya bayyana cewa an cafke Florence Karakacha ne bayan ta lakaɗawa mijinta mai suna Bramwel Lubanga dukan tsiya saboda ya ƙaro aure.
Lubanga ya rasa wani ɓangare na leɓen sa bayan matar ta cije shi yayin da suke taƙaddamar. Matar ta cinnawa gidan wuta kafin na n ta garzaya zuwa ofishin ƴan sanda.
A ofishin ƴan sandan tayi zargin cewa mijinta shine ya fara afka mata daga farko.
Nan da nan cikin gaggawa jami’an ƴan sanda suka zo suka tasa ƙeyar Lubanga zuwa ofishin su.
Sai dai bayan an samu bayanai daga wajen makwabta da ƴan’uwa, ƴan sanda sun gano cewa Florence ta lakaɗawa Lubanga duka ne bayan ya ƙaro aure bayan ya fahimci cewa tana cin amanarsa ta hanyar yin lalata da ɗan’uwan sa.
Nan da nan sai reshe ya juye da mujiga inda aka cafke ta sannan aka tsare ta har zuwa lokacin da za a miƙa ta a gaban kotu.
Tsoho Ɗan Shekara 71 Ya Mutu Yana Tsaka Da Goge Raini Akan Gado Da Wata Budurwa
A wani labarin na daban kuma, wani tsoho yace ga garin ku nan yana tsaka da goge raini akan gado da wata budurwa mai jini a jika.
Wani tsoho ɗan shekara 71 ya kwanta dama yana tsaka da goge raini akan gado da wata budurwa ƴar shekara 22 a duniya.
Lamarin dai ya auku ne a wani masaukin baƙi a Parklands, birnin Nairobi na ƙasar Kenya.
Tsohon wanda ya shiga cikin ɗakin da wajen misalin ƙarfe huɗu na yamma, ya fara neman iska sa’o’i biyu bayan shigar su ɗakin, sannan yayi ƙorafin yana jin ciwon ƙirji da na baya.