Wani tsoho ɗan shekara 71 ya kwanta dama yana tsaka da goge raini akan gado da wata budurwa ƴar shekara 22 a duniya.
Lamarin dai ya auku ne a wani masaukin baƙi a Parklands, birnin Nairobi na ƙasar Kenya. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Al-Nassr Ya Gwangwaje Cristiano Ronaldo Da Wata Gagarumar Kyauta
Tsohon wanda ya shiga cikin ɗakin da wajen misalin ƙarfe huɗu na yamma, ya fara neman iska sa’o’i biyu bayan shigar su ɗakin, sannan yayi ƙorafin yana jin ciwon ƙirji da na baya.
Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kawai sai hannayen sa da ƙafafun sa suka daina motsi, wanda hakan ya sanya budurwar ta gaggauta kiran wani direban tasi wanda yake tsaye a ƙofar shiga ginin.
An garzaya da shi zuwa asibitin Agha Khan inda yake tabbatar da cewa ya mutu.
Tuni dai aka miƙa gawar tsohon zuwa ɗakin ajiyar gawarwaki kafin zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Sabon bincike ya nuna cewa aƙalla duk namijin Ƙasar Kenya yana lalata da mata 7 kafin ya mutu
A wani labarin na daban kuma, wani sabon bincike ya bayyana adadin matan da mazajen Kenya ke lalata da su kafin su mutu.
Wani sabon bincike da Kenya National Bureau of Statistics (KNBS) ta saki ya nuna cewa kowanne namiji a kasar Kenya yana lalata da akalla mata 7 a tsawon rayuwarsa, mata kuma maza biyu.
Kamar yadda rahoton mai taken “Kididdigar Yanayi da Lafiya”, ya nuna, kaso 35 na maza cikin watanni 12 akalla suna saduwa da matan da ba matansu ba kuma ba ‘yan matansu ba idan aka hada da kaso 19 na mata.