Ƴan Ƙungiyar Awaren Inyamurai ta IPOB ta baiwa Gwamnan Jahar Imo Hope Uzodinma wa’adin kwanaki ya sako mambobin ta da aka kama a Jahar, ko kuma ya fuskanci fushin su.
IPOB ta baiwa Uzodinma ƙarshen watan Nuwamba ya sako mata mambobin ta, wanda jami’an tsaro suka kama a Jahar Imo.

KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Anambra: Dan Takarar Gwamna Ya Kadawa Soludo Kuri’a
Mai magana da Yawun IPOB Emma Powerful yayi gargaɗin haɗa gangamin mutane a yankin Kudu Maso Gabas domin su ƙalubalanci Uzodinma, idan har bai sako mata mambobin ta ba.
A cewar Powerful “muna so muyi magana akan sace mana mambobi da ake yi, wanda jami’an tsaron Najeriya keyi ƙarƙashin jagorancin Shugaba a Imo Hope Uzodinma, Yana mai cewa bai isa ya hana su neman a basu yankin su ba, kasancewar Imo na cikin Ƙasar Biafra.
Ƙungiyar Ƴan Awaren ta buƙaci Shuwagabannin Inyamurai da Sauran Shuwagabanni dasu matsa lamba ga Uzodinma ya sako masu mambobin su da aka kama.