Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi watsi da yarjejeniyar karshe tsakanin G5 da yake jagoranta da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Tsagin G5 ya kunshi Wike, Samuel Ortom (Benue), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia), da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu).
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Gwamnonin na PDP da suka fusata sun fice daga yakin neman zaben Atiku, inda sula bukaci Sanata Iyioricha Ayu ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar na kasa a matsayin shuradin komawarsu.
KARANTA HAKANAN Wike Ya Bayyana Abunda Suka Tattauna Da Atiku Tinubu Da Obi
Sai dai jam’iyyar PDP ta gudanar da yakin neman zabenta ba tare da aniyarsu ba, inda ta kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a Oyo, ba tare da sa hannun Makinde ba.
Da yake magana a wata tattaunawa da manema labarai a safiyar Alhamis, Wike ya kawar da duk wata tattaunawa da shugabannin PDP.
“A’a, ba za mu iya yin haka ba; an kare! Mun fadi hakan kuma babu wani abu da kowa zai iya yi game da shi yanzu. Suna ganin za su iya lashe zaben. Ban shirya sake zama da kowa ba,” in ji gwamnan yayin da yake amsa tambayar.
Wike ya bayyana haka ne sa’o’i bayan da ya karbi bakuncin Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a gidan gwamnati da ke Fatakwal, a halin da ake ciki Atiku ya soke taron da zai yi a Rivers, saboda dalilan tsaro.
Tinubu ya ziyarci Wike ne bayan yakin neman zabe a filin wasa na Yakubu Gowon, wanda har yanzu yake a Fatakwal.
Da yake magana yayin ziyarar ta Tinubu, Wike ya ce, “Ba ni da uzuri ga kowa da ya ce babu wanda mace ta haifa da zai iya tsoratar da ni. Ba ka taba canza jam’iyya ba wata rana. Wannan ya bayyana halinku da jajircewarku kuma abin da muke bukata ke nan a kasar nan.”
Da yake tsokaci kan ziyarar Tinubu a taron manema labarai na ranar Alhamis, Wike ya ce ba shi da wani uzuri na karbar dan takarar shugaban kasa.
Wike da Tinubu sun yi yarjejeniya a kasashen waje domin kammala dabarun zaben 2023, kamar yadda majiya ta bayyana, amma bangarorin biyu sun musanta rahoton.
Jaridar Daily trust ta rawaito cewa Tinubu ya gudanar da tarurruka daban-daban da Wike yayin da ake tunkarar zaben 2023 yayin da manyan jiga-jigan APC suka kaddamar da ayyukan da gwamnatin Wike ta aiwatar.
A Wani Labarin Kuma Amurka Za Ta Dawo Da Dala $954,000 Da Tsohon Gwamnan Bayelsa Ya Sace
Kasar Amurka da gwamnatin tarayya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya maido da dala 954,000 da tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Diepreye Alamieyeseigha ya sace.
Jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Beth Leonard ce ta sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka yi da yammacin ranar Alhamis din nan a Abuja.