Kotun shari’ar musulunci mai zaman ta a filin Hoki a jihar Kano, ta bayar da umurnin a cigaba da tsare shahrarriyar ƴar dandalin TikTok, Murja Ibrahim Kunya, a gidan gyaran hali.
Kotun ta bayar da wannan umurnin ne a yau Alhamis, 16 ga watan Febrairu, a yayin da ta cigaba da sauraron ƙarar d ake yiwa Murja bayan ta gurfana a gabanta. Rahoton jaridar Hausa.Legit
KU KARANTA KUMA: Ana Dab Da Ɗaura Musu Aure, Matashi Ya Ritsa Budurwarsa Na Cin Amanarsa a Otal
Alƙalin kotun shari’ar musuluncin yayi umurnin a mayar da Murja Ibrahim Kunya gidan gyaran hali da tarbiyya har zuwa nan da mako guda.
Murja dai har ila yau ta musanta tuhumar da ake yi mata a gaban kotu.
Lauyan Murja ya nemi kotu da ta bayar da belin ta, amma lauyan gwamnati ya ƙi yarda da hakan inda ya nemi da a bashi sati guda domin yayi martani.
Kotun ta tura Murja zuwa gidan yari har zuwa 23 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Dangane da tuhumar da aka soma yiwa Murja a zaman da ya gabata kuwa, Murja ta rubuto takardar cewa ta tuba.
Kotun ta ce za ta yi nazari a zaman ta na gaba
An Gano Tsohuwa Ƴar Shekara 150 a Najeriya, Bidiyonta Ya Ɗauki Hankula
A wani labarin na daban kuma, bidiyon wata tsohuwa ƴar shekara 150 a duniya, ya ɗauki hankula.
An gano wata tsohuwar mata mai shekara ɗari da hamsin a duniya, wacce har yanzu tana da kyawunta a Najeriya.
Wata matashi mai gudanar da cibiyar Joy Peters Foundation da kuma bayar da kayan jin ƙai ga marasa ƙarfi, itace ta ziyarci tsohuwar.