Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce gwamnatinsa ta samu rahoton sirri da ke nuna cewa ‘yan siyasa a jihar sun fara daukar ‘yan kungiyar asiri da kuma wadanda aka yankewa hukunci domin a yi amfani da su a matsayin ‘yan bangar siyasa kafin da kuma lokacin babban zaben shekara mai zuwa.
Gwamna Wike a wata kafar yada labarai na jihar ya ce rahotannin sun kuma nuna cewa ana gudanar da tarurrukan daukar ma’aikata a otal-otal da sauran wuraren nishadi da ke kewayen jihar.
Ya kuma yi gargadin cewa gwamnatin sa ba za ta bar wani dan siyasa ba, duk da matsayinsa na baya ko na yanzu ko ra’ayinsa na siyasa ya tada zaune tsaye da jami’an tsaro suke ta kokawa a jihar Ribas.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/peter-obi-yayi-ganawar-sirri-da-fayose-na-jamiyyar-pdp/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Gwamna Wike, ya yi gargadin daukar tsauraran matakai kan wadanda suka aikata laifin, yana mai cewa gwamnatinsa za ta “rushe duk wani otal ko wuraren shakatawa da ake gudanar da irin wadannan tarukan”.
Gwamnan jihar Ribas ya kuma bayyana cewa an sanar da jami’an tsaro don bin diddigin wadannan ‘yan siyasa da ake zargi da daukar ‘yan baranda.
Ya yi kira da a kara sanya ido a tsakanin mazauna yankin tare da gode musu bisa goyon bayan da suka ba su tun hawansa ofis a shekarar 2015.
(Channels TV)