Tsohon Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, yana da damar ganawa da kowa ko kuma ya yi hulda da duk wanda yaso.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa, Kola ya ce Wike zai yi hakan ne, matukar bai dauki katin zama dan wata jam’iyyar siyasa daban da PDP ba.
Ologbondiyan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata hira da aka yi da shi a cikin shirin ‘The Morning Show’ na gidan talabijin din Arise.
Ya bayyana cewa ba shi da wata matsala da Wike don haka ya gana da duk wani wanda yake da ra’ayin ganawa da shi, daga wata jam’iyyar siyasa.
Wannan jawabi na Tsohon sakataren jam’iyyar na zuwa ne, bayan da yake amsa tambayoyin da suka shafi ganawar Wike da ‘yan siyasa daga wasu jam’iyyun siyasar kasar.
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Wike ya gana da wasu gwamnonin jam’iyyar APC, da suka hada da gwamnan Legas, Ondo da Ekiti, Babajide Sanwo-Olu, Rotimi Akeredolu da Gwamna Kayode Fayemi.
Haka kuma a kwanakin baya ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, wato Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, a daren Litinin.