Wani bidiyo da ya nuna lokacin da wani ango ya kama sharɓar kuka, ya yaɗu sosai a manhajar TikTok.
A cikin bidiyon angon ya ƙasa ɓoye shaukin da angon yake ciki wanda hakan ya sanya shi zubar da hawayen farin ciki. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Yan Sanda Na Gudanar Da Binciken Hallaka Wani Jami’i Da Soja Ya Yi
Amaryar sa ta ji dadin abinda ya faru wanda hakan ya sanya ta ta yi ta washe baki tana murmushi.
Mutane da dama da suka kalli bidiyon mai sosa zuciya sun yi nuni da cewa tsananin shaukin da angon yake ciki ne wanda suka kasa gane ko na menene.
Bidiyon ya yaɗu sosai inda mutane da dama suka yi sharhi a kan sa, sannan wasu da yawa kuma suka danna masa alamar ‘like’.
Ku kalli bidiyon a nan
“Sam Ba Zan Iya Auren Mace Mai Daukar Albashin N5m”, Matashi Ya Bayar Da Dalilan Sa
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya bayyana dalilan da za su sanya ya ƙi auren mace mai ɗaukar albashin N5m.
Wani matashi ɗan Najeriya yace ba zai iya auren matar da take ɗaukar albashin naira miliyan biyar (N5m) ba a wata.
Matashin ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo, yayin da wata budurwa take masa tambayoyi.
Comments 1