Wata Matashiya a Najeriya ta bayyana irin halin da wata kawarta ya shiga bayan wani damfarar kalamai da wani saurayi ya yi mata lokacin suna nema.
Matashiyar mai suna Fairy Gbemie ta bayyana cewa mijin kawar tata ya sharara mata karyar cewa shi dillalin motoci ne, to amma bayan sun yi aure ta gane cewa ashe Makanike ne.
Ko da yake bata bayyana sunan kawar tata ba, amma bisa la’akari da Kalamanta ta nuna cewa yana zirga-zirga cikin motoci daban-daban lokacin da yake zuwa wurin ta.
Duk da cewa har kawo yanzu ba ta bayyana tsawon lokacin da suka shafe a tare ba, amma galibin jama’a na hasashen cewa wannan aure ba lallai ne ya yi karko ba.
Da ma dai a irin wannan zamani yan mata da dama na kasancewa ne a sahun ma’abota samun wurin hutu a rayuwarsu ta aure, to amma an ce tabbas idan da kwadayi lallai akwai wulakanci.
Muna sakawa kanmu karya ne a rayuwarmu shiyasa muke da azzalumai na mulkammu akasar Nan tamu Nigeria
To wanan jarini yanuna jarimta kwarai da gaske, saboda be bar soyayar shi ta tafi a banza ba kuma shi ya lura kwadayayiya ce kuma mace mai kwadayi batason gaskiya ko kadan
Oh ashe badon Allah kika aureshiba don yace shi Dillalin motoci ne yasa kika aureshi hmm
Kwadayi mabudin wahala, ya fahimci idan ya gaya mata gaskiya bazata aminta bane yasa ya biyo ta wannan sigar. Abin jan kunnen anan shine kigayawa kawartaki ta tsaya kan gaskiya zata samu miji nagari ko mai dukiya ko marar dukiya, domin dukiya ba itace farin cikin ma’aurata nuna so da kulawa shine abin bukata. Daga karshe ina fatan wannan zai zama darasi ga sauran matan da suke da kudirin cewa sai mai kudi zasu aura.