By Abbas Yakubu Yaura
Kwamishinan Muhalli na Jihar Kogi, Cif Victor Adewale Omofaiye, yace ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin yin garkuwa da shi da akayi a kan hanyar Ikoyi-Iyara a ranar 28 ga watan Nuwamba.
Kwamishinan ya fadi hakan ne a Lokoja ranar Asabar a wata ‘yar gajeriyar hira da manema labarai, yayin da ya godewa Allah da ya tsare rayuwarsa daga fadawa hannun masu garkuwa.
Ya ce ya yi imani da gafara, don haka ya gafarta wa wadanda suka yi yunkurin yin garkuwa da shi, inda ya bukace su da su tuba daga munanan ayyukansu.
Sannan ya bukaci al’ummar jihar da su rungumi zaman lafiya da soyayya da kuma hakuri da juna yayin da mabiya addinin kirista ke bi sahun sauran kasashen duniya domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti.