Real Madrid ta gabatar da tayin fam miliyan 137 a kan dan gaban Paris St-Germain Kylian Mbappe, amma kuma kila kungiyar ta Faransa ta yi watsi da tayin na dan wasan mai shekara 22, wanda ke da ragowar shekara daya a kwantiraginsa. Inji jaridar (Mail).
Watakila PSG ta nemi sayen dan gaban Everton da Brazil Richarlison, mai shekara 24, a matsayin wanda zai maye gurbin Mbappe. Cewar jaridar (Eurosport)
Dan gaban Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, zai nemi tafiya Manchester City a cikin makon karshe na kasuwar sayar da ‘yan wasa, domin tsohon dan wasan na Manchester United ba shi da sha’awar kamala ragowar kwantiraginsa a kungiyar ta Italiya.
City a shirye take ta biya albashin da Ronaldo zai nema amma kuma ba lalle ba ne ta yarda ta biya yawan kudin da za a san a farashinsa ba. (L’Equipe)
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NAPTIP ta ceto Mutum 104, tare da cafke Mutum 8 da ake zargi
A gefe guda kuwa, Manchester United na gaba-gaba wajen damar sayen dan wasan gaba na Borussia Dortmund da Norway Erling Braut Haaland a bazara ta gaba. Dan wasan na Norway mai shekara 21 ya zama daya daga cikin wadanda kungiyoyi ke rububin nemansa bayan da ya ci wa kungiyarsa kwallo 62 a wasa 63. (Bild)
Har’ilayau Chelsea ka iya fuskantar gogayya daga Manchester United idan ta tashi tsaye, domin daukar aron dan wasan tsakiya na Atletico Madrid da Sifaniya Saul Niguez, mai shekara 26 cewar jaridar (Guardian).
Atletico Madrid na da niyyar daukar dan wasan tsakiya na Sifaniya Pablo Sarabia mai shekara 29 daga Paris St-Germain idan Saul ya tafi. (Marca)
Itama kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta tattauna da Atletico Madrid a game da sayen dan bayan Ingila Kieran Trippier, ko da yake dan wasan mai shekara 30 zai fi son tafiya Manchester United idan ya bar babban birnin na Sifaniya. Arsenal ba za ta yarda ta sayi tsohon dan bayan na Tottenham ba a farashin da Atletico ta yi masa fam miliyan 34 ba. (Eurosport)
Comments 1