Wata budurwa mamba a hukumar yi wa kasa hidima NYSC a halin yanzu ta fara jan hankula saboda kwarewarta ta wasan kwallon kafa, Legit.ng ta rawaito.
Budurwar ta yi kyau sosai, da ta dauko kwallon ta yi wasa da ita, sai ga maza suka tsaya sekeke suna binta da kallon salon yadda take lelaya kwallo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Atiku Ya Yi Al’ummar Kogi Wani Mahimmin Alkawari Idan Ya Lashe Zabe
Bidiyon budurwar wanda aka sanya shi zuwa kafar sada zumunta ta Instagram kuma a halin yanzu yana ci gaba da janhankulan jama’a inda jama’a fiye da dubu 39k suka yi likes da yawa na godiya.
Budurwar mai yi wa kasa hidima ta NYSC ta samu karbuwa ta yanar gizo saboda yadda ta kware a harkar kwallon kafa.
Yarinyar ta dauko kwallon ne a tsakiyar ’yan kungiyar masu yiwa kasa hidima maza kuma ta rike su da gwaninta.
Lokacin da ta fara tseren ƙwallon, ta bayyana a fili cewa ta ƙware. Yan kungiyar masu yiwa kasa hidima mazan sun tsaya suna kallo cike da mamaki.
Wata mace da ta bayyana ita ce ta ɗauki hoton lokacin da ƙwararriyar ‘yar wasan ƙwallo da ake kira ‘agba baller’.
Ta dade da rike kwallon tana wasa da ita bata fado daga kafarta ba sai da tayi niyyar sauke kanta cikin salo.
Masu amfani da Instagram, ciki har da ƙwararrun mata masu buga ƙwallon ƙafa, Desire Oparanozie ta yaba wa mamban ƙungiyar saboda basirar ta. An fara sanya bidiyon akan TikTok na mai amfani dashi 22550104.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Gobara Ta Tashi A Hedikwatar ‘Yan Sandan Jihar Kano
Yanzu haka dai gobara ta kone wani katafaren sashin gudanarwa a hedikwatar ‘yan sanda da ke Kano.
Bayani game da lamarin yana da tsari kawo lokacin gabatar da wannan rahoto.