Osifo Kyiri Osofo Kyiri Absom ya bayyana wa tsohuwar matarsa cewa yana da damar dirka wa duk yawan matan da ya ga dama ciki, Musbizu.com.ng ta ruwaito
Wannan ya biyo bayan yadda aka samu zargi kan ya yi lalata da mata da dama kuma duk babu wacce bai haihu da ita ba.
KU KARANTA: Saka rigar bacci asarar lokaci ne saboda da safe za ki tsince ta a ƙasa, Fasto ga matarsa
Ya zargi tsohuwar matarsa da rashin mutunta shi tare da yada karairayi akan shi yayin da ake ganin darajarsa a matsayinsa na fasto.
Osofo Kyiri Absom bai bayyana cewa aurensu ya rabu ba kawai, ya kuma ba kansa damar auren duk matan da ya ga dama.
Ya yi ikirarin cewa yana da damar kara yawan mata, cikin masu zuwa cocinsa ga sauran yawan matan da ya ajiye a gida.
Kuma ya ce matarsa bata isa ta dakatar da shi daga yin abubuwan da ya ga dama ba.
Kamar ya ce:
“Idan ina so, zan iya saka wasu daga cikin ku a jerin matana. Aikin babba ne amma kuma a hankali lokaci ma kara tafiya ina kara yawan mata. Kuma ina da damar yin hakan kuma zan yi.”
A matsayinsa na mutumin da ke kusa da Ubangiji ya ce zai ma iya dirka wa duk matar da ya ga dama ciki.
Na ji ‘yan wutar Jahannama suna wata fitacciyar wakar mawakiya Rihanna, Fasto
Fitaccen fasto Gerald Johnson, wanda ya mutu na wucin gadi ya janyo cece-kuce kala-kala a kafafen sada zumuntar zamani, Legit.ng ta ruwaito.
A cewarsa kamar yadda ya bayyana a shafinsa na TikTok, bayan ya yi mutuwar wucin gadi sakamakon bugawar da zuciyarsa ta yi a Fabrairun 2016, ya ji wani abin ban mamaki.
Ya ce ya ji yadda azabar wuta yake don haka ba zai taba yi wa wani fatan shiga wutar ba. Sannan akwai wani yanki da ke wuta wanda ‘yan wuta ke sauraron wata wakar da ke duniya mai suna Umbrella ta mawakiya Rihanna da kuma Don’t Worry Be Happy ta Bobby McFerrin.