Wata ‘yar Najeriya mai suna Kulu Hauwa’u Adam Usman Alaket, ta rasu ana gab da daurin aurenta.
KU KARANTA: ‘Yan sanda sun ceto shugaban kotu, jami’i daya ya rasa ransa
Kamar yadda bayanai suka nuna, an kammala duk wasu shirye-shiryen aurenta, saidai kuma mutuwa ta yi saurin dauke ta.
‘Yar uwarta ta bayyana cewa a ranar Asabar, 14 ga watan Janairun 2023 ne aka tafka hatsarin a karamar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato.
Dama an tsara za a daura aurenta ne da saurayinta, Aliyu Usman Fulani a ranar Juma’a, 27 ga watan Janairu a Jihar Filato.
Wannan lamarin ya yi matukar daukar hankula sosai wanda tuni ‘yan uwa, masoya da abokan arziki suka garzaya inda suka dinga mika ta’aziyya ga ‘yan uwanta.
Shakka babu, ana tunanin angon nata ya shiga damuwa matsananciya, amma babu yadda aka yi, tunda lokacin ta ya yi.
Mutane Biyu Sun Jikkata Yayin Da Wata Mata Ta Rasa Ranta A Hatsarin Mota A Jos
A ranar Alhamis din data gabanta ne aka tabbatar da mutuwar wata mata a wani hatsarin mota da ya afku a unguwar Babale da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.
An tattaro cewa wasu biyu sun samu raunuka kuma an garzaya da su asibitin kwararru na jihar Filato da ke birnin Jos.
Wasu Shaidun gani da ido sun bayyana cewa hatsarin wanda ya rutsa da wata motar tanka da kuma babur mai Keke Napep ya afku ne da misalin karfe 4 na yamma.