Wani bidiyo ya bayyana yadda rigima ta barke tsakanin wata karuwa da wani dattijo bayan ya yi lalata da ita bai biya ta kudi ba ya yadu a kafafen sada zumunta, LIB ta ruwaito.
Matar wacce ta dinga daga murya tana hargowa da kwastomanta wanda da alamu ya kai shekaru 50 zuwa sama.
KU KARANTA: Yadda matasa 3 suka garzaya gidan karuwai suka zaɓi tsala-tsalan mata suka aura
Yayin bayyana yadda lamarin ya auku, karuwar ta ce dattijon ya nemi su yi lalata na dare gabadaya amma sai ya biya ta na karo daya.
Daga bisani ta kwace wayarsa bayan ya ki biyanta kudin. Yayin da mutumin ya ki barin wayarsa, ta lashi takobin kawo ‘yan daba inda za su ja masa bala’i.
Sauran ‘yan haya suka dinga rokonta kan idan ta gayyaci ‘yan daban su daki mutumin shi kadai saboda su ba su da laifi.
Yadda karuwa ta lakaɗa wa abokiyar sana’arta na jaki kan yi wa kwastomomi rahusa
Wata karuwa tana gaban kotu bayan lakada wa abokiyar sana’arta na jaki kan amsar kudi kasa da yadda suka yi yarjejeniyar amsa daga kwastomomi.
Mariam Imodia ta bayyana gaban kotun majistaren Mombasa, wanda a gaban alkali Vincent Adet ta amsa laifin azabtar da Gladys Ahela.
An samu bayani kan yadda Ahela ta koma yankin Saba Saba da ke Mombasa Central Business District (CBD) a Kenya, bayan wasu kwastomomi da suka kai mata ziyara.