Wata mai kwalliya ta wallafa kwalliyar da ta zage damtse wurin yi wa kwalliya amma lamarin ya faskara don bata sauya ba ko kadan, kamar yadda ta wallafa a shafin masu kwalliya mai suna Makeup Artists da ke Facebook.
Daga ganin tsohuwar ta zarce shekaru 70 a duniya kuma duk fatarta ta yi yaushi saboda yawan shekaru.
KU KARANTA: Tsohuwar kwamishina Ibim Semenitari ta fice daga APC zuwa PDP
Sai dai da alamu tsohuwar bata yarda a bar ta a baya ba a duniyar gayu don ta tsaya ayi mata kwalliyar zamani.
Duk da dagewar mai kwalliyar, lamarin ya faskara don babu abinda bata shafa ba amma yadda tsohuwar ta ke, tana nan babu sauyi.
Mutane da dama sun yi ta tsokaci karkashin jerin hotunan wadanda ta fara dauka kafin ta fara kwalliyar har zuwa sanda ta kammala.
Wasu na ganin dama haka ta bar ta ba tare da wahalar da tsohuwar ba.
Kotu Ta Dakatar Da EFCC Daga Kwace Kadarorin London Dake Da Alaka Da Tsohuwar Minista Diezani
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Maitama birnin tarayya Abuja ta hana Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa EFCC karbe wasu kadarori hudu a Landan da ke da alaka da tsohuwar Ministar Man Fetur, Misis Diezani Allison-Madueke bisa kuskure.
Kotun, a wani hukunci da mai shari’a Olukayode Adeniyi ya yanke, ta kuma haramtawa babban mai shigar da kara na tarayya, da hukumar kare laifuffuka ta kasa (UK), da kuma wasu masu binciken Burtaniya uku- Helen Hughes, Stacey Boniface da John Bavister- daga kwace kadarorin.
Mai shari’a Adeniyi ya bayyana cewa, shaidun da ke gaban kotun sun tabbatar da cewa kadarorin da aka ambata a bisa ka’ida mallakar wani hamshakin attajiri ne, Mista Benedict Peters da kamfanoninsa.