Wani Hamshaƙin Ɗan kasuwa a Jahar Rivers Alex Arthur, ya bayyana yadda ya ciyar da wani yaro, ya kuma tufatar shi amma ya haɗa kai da wata tawagar masu garkuwa da mutane, domin sace shi a Fatakwal dake Jahar Rivers a ranar 8 ga watan Satumba.
Alex Arthur ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar inda yace “akwai wani yaro dake zama a gida na dana baro. Sunan sa Golden da akafi sani da Sugar Gold. Na haɗu dashi a farkon shekara. Kuma na ɗauke shi har sai da ya zama ina ɗaukar ɗawainiyar shi.
“Ina taimaka mashi kuma ina tufatar dashi. Na nuna mashi soyayya duk da bamu da alaƙa dashi. Amma shine wanda ya hada baki da ƴan ta’adda domin su sace ni.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Benue: Jami’an Tsaro Sun Cafke Sarkin ‘Yan Bindiga Azonto
Dayake jawabi yadda aka so satar shi, Alex yace yana akan hanyar shi zuwa wajen motsa jiki, sai yaci karo da wata tawagar mutanen da suke son sace shi, suka tunkaro shi.
“Sun zo a wajen buɗe kofa, wasu matasa guda biyu suka tunkaro ni, ɗaya ya nuna mani ID card cewa shi sojan ruwa ne, kuma ya kira suna na, da lambar waya, da ƙaramar hukuma ta, ya kira dukkanin bayanan da suka bayyana koni waye.
Ɗayan matashin ya futo da bindigar sa, tare da tambaya ta da in koma bayan kujerar mota ta, wani kuma ya hau saman inda nake tuƙi.
Sun bi kan hanya, inda wani daga cikin su ya shiga wani ofishi ya karɓo wasu kayayyaki, tare da zuwa banki, inda ya gudanar da wasu al’amura na kuɗi.
Yace ɗaya daga cikin su yana tsare dashi da bindiga a lokacin da yake bayan kujerar.
“Daga nan suka kaini wani yanki da bansani ba a iyakar Oyigbo, inda suka ajiye ni tare da buƙatar in basu Naira miliyan 1.5. Bayan mun tattauna, sai suka ce ban fito da wasu kuɗade masu yawa. Sai suka ajiye ni a bayan gidana inda suka tafi da talabijin da kwashe kayan dake Firiza ta.
Sun tafi da kayayyakin da suka haɗa da mota ta, waya ta, talabijin da Naira dubu ɗari 128,000 da kuɗaɗe masu yawa da sauran su.
Yace bayan ƴan sanda sun bi kadin wayar sun kama su, inda suka ce Sugar Gold ne ya turo su domin su kama shi.
“Naji babu daɗi cewa wanda nake taimaka mashi, amma shiya dawo yake neman kashe ni. Mutane suna ta neman in yafe mashi, na yafe mashi amma zai fuskanci abunda ya shuka.