Yadda na kashe ma’aikacin gidan Super Tv
An cafke wata daliba yar makarantar Jami’ar Legas mai suna Chidinma Ojukwu kan kisan Mr. usifo Ataga Babban mai kula da gidan talabijin na Super Tv, Kuma ta bayyana dalilinta na kanyin hakan.
A lokacin da take magana a cikin gidan Yan sanda tace ka caka masa wukane yana kokarin kwantawa da ita.
KARANTA:- Hukumar EFCC ta cafke mutane uku da laifin damfara 3.5 Biliyan
Ma’aikatan labarai sun ce an gano gawarsa ne tare da ciwuka a Lekki Phase 1 dake Legas.
An kama daliban ne a unguwar su dake Alagomeji dake Yaba inda take zaune ita da iyayenta, sannan tace sun hadu da Ataga watanni biyar da suka gabata.
A ranar Lahadi 13 ga watan June yace na sami wurin da zamu zauna da naje na duba, naje na duba sannan na biya kudin.
A ranar Litinin 14 ga watan June muna tare dashi muna cin abinci muna shan abun sha, a ranar Talata 15 ga watan June ya fara kusanta ta na dai nuna masa a.a sai ran sa ya baci ya kama fada sai ya tafi.
Na koma gefe ina kallon talabijin sai ya kara zuwa nace masa a.a don bana jin raayin hakan nace masa Kai baka taimako na kuma kanason Kai amfani dani, ya cigaba da kusan toni amma Ina Kare kaina.
Har dai takai da ya buga kaina da kasa Ina kokarin guduwa amma kofar a kulle take shi kuma yana jawoni baya.
Tace sai na dauko wuka a dakin girki ma caka masa sau biyu a wuya sannan na jefa wukar saman gado yana kokarin daukar wukar na sake dauka na kara caka masa.
Tace bayan ta fita sai ta cire kudi 380,000 daga asusun Ataga ba miliyan biyar ba.