An bukaci wani mutum yayi rainon yaransa inda ya gajiya har ya bige da kwashewa da bacci su kuma yaran su ka mike su ka dinga hargitsa gidan tare da wasanni, Legit.ng ta ruwaito.
Da alamu ya gaji da kulawa da yaran ne hakan yasa ya samu kujera ya dinga sharar bacci.
KU KARANTA: Dalilin da yasa tsarin kiwon lafiya matakin farko ba ya aiki yadda ya kamara, FG
Wannan bidiyo ya yi matukar daukar hankalin mutane inda ya dinga yawo a kafar TikTok.
Mutane da dama sun dinga tsokaci a karkashin bidiyon wanda aka wallafa ranar 19 ga watan Nuwamba, inda aka ga mutumin yana ta sharar bacci.
Bidiyon ya kai sakanni 17 inda shafin Martin Family ya wallafa inda aka ga yaran su na wasanni da kwando yayin da babansu ke sharar bacci.
Da alamu ya gaji ne, sai ya killace su sannan ya baje a kujera ya dinga sharar bacci.
Mutane da dama sun dinga tsokaci iri-iri karkashin bidiyon wanda mamarsu ta yi amfani da damar nan ta yi kira ga iyaye maza.
Na Yi Farin Cikin Cewa Mata Na Da Fatan Sake Fasalin Najeriya — AA
Dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abukakar Wazirin Adamawa ya ce mata suna da rawar da zasu taka wajen cigaban kasar nan.
Atiku ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da majalisar yakin neman zaben shugaban Kasa bangaren Mata a ranar Larabar nan.
Da yake jawabi ga majalisar yakin neman zaben ta Mata ya bayyana farin ciki tare da murnar cewa Mata suna fatan sake fasalin Kasar nan duba da yadda suka taro a wannan taro.