Zargin Cushe: Majalisar Dattawa na duba yiwuwar warware dakatarwar da ta yiwa Ningi – Akpabio
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa majalisar za ta dawo da Sanata Abdul Ningi daga dakatarwar da aka yi masa na tsawon watanni uku.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a lokacin da ya isa wurin taron kungiyar ‘yan majalisar dokokin kasa a birnin Geneva na kasar Switzerland.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Bauchi Ta Bada Tallafin Karin Kuɗin Aikin Hajji Da Kashi 50%
Akpabio ya ce nan ba da jimawa ba majalisar dattawa za ta sake duba dakatarwar da ta yi wa Ningi na tsawon watanni uku saboda ikirarin cewa an yi wa kasafin kudin shekarar 2024 Cushe na makudan kudade har naira tiriliyan 3.7.
DAILY POST ta tuna cewa Ningi a ranar Alhamis, a wata wasika da lauyansa, Femi Falana SAN ya rubuta, ya bukaci a mayar da shi majalisar dattawa.
Akpabio ya yi nuni da cewa duk da bai ga wasikar dakatarwa ba, za a warware matsalar tunda ta cikin gida ne.
Ya ce: “Hukuncin majalisa ne. Har yanzu ban ga wasikar dakatarwa ba. Amma Sanata Ningi yana daya daga cikin mu. Ina nufin, menene dakatarwa.
A wani labarin kuma:Yadda wani matashi ɗan jihar Bauchi ya caka wa wani abokinsa wuƙa
Wani bala’i ya afku a karamar hukumar Ningi da ke jihar Bauchi yayin da Adamu Isa dan shekara 15, dan wani jami’in dan sanda mai ritaya, ya caka ma abokinsa wuƙa Abubakar Isa.
An ce lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris bayan wata zazzafar cece-kuce tsakanin abokanan.