Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke wani matashi mai shekara 22 a duniya, mai suna Muhammad Bala, wanda ya fito daga Mararaba-Madagali cikin ƙaramar hukumar Madagali, bisa zargin halaka wani abokin takarar sa.
Ana zargin Muhammad Bala da halaka wani matashi mai suna Bakura, wanda suke neman wata budurwa da niyyar aure tare. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: FG Ta Daga Likafar FMC Lokoja Zuwa Asibitin Koyarwa
Wanda ake zargin dai ya aikata laifin ne a ranar 15 ga watan Fabrairun 2023, da misalin ƙarfe tara na dare a gidan su budurwar mai suna Maryam Muhammad bayan zazzafar gardama ta ɓarke a tsakanin su.
Lokacin da ƴan sanda ke tuhumar sa, wanda ake zargin ya bayyana cewa da shi da abokin takarar ta sa sun sha samun saɓani a baya sannan sun ja kunnen junan su kan su daina zuwa wajen Maryam.
An samo cewa ranar da lamarin ya auku, matasan biyu sun haɗu a gidan su yarinyar inda rigima ta ɓarke a tsakanin su.
Rigimar ta rikiɗe ta koms faɗa, wanda ana cikin hakan kawai sai wanda ake zargin ya cakawa marigayin wuƙa wanda ya rasu daga raunikan da ya samu.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, yace za a tura wanda ake zargin zuwa kotu da zarar sun kammala bincike.
“Daga Cewa Su Gaisa Sai Ta Ƙwace Shi” Budurwa Ta Koka Bayan Ƙawarta Ta Ƙwace Mata Saurayi
A wani labarin na daban kuma, wata budurwa ta koka kan yadda ƙawarta tayi mata ƙwacen saurayi.
Wata mata ta koka kan yadda ƙawarta tayi mata ƙwacen saurayi bayan ta haɗa su.
Matar mai suna Munira ta sanya wasu bidiyoyi waɗanda suka nuna irin kusancin dake tsakanin su da ƙawarta wacce tayi mata cin amana.