Kungiyar daliban Najeriya ta kasa a ranar Talatar da ta gabata ta yi kira ga ministan ilimi Mista Adamu Adamu ya yi murabus saboda yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ke cigaba da yi
Punch ta ruwaito cewa, Shugaban na NANS ya bayyana haka ne a yayin zanga-zangar da ta gudana a kan titin Legas zuwa Ibadan bisa zargin cewa ministan bai nuna sha’awar tattaunawa da kungiyar ASUU don janye yajin aikin ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda Sun Gano AK-47, Da Harsasai Da Aka Buye A Keke Napep
Da yake zantawa da wakilin Majiyar Dimokuradiyya, Mataimakin Shugaban NANS (Ma’aikatar Harkokin Waje), Akinteye Babatunde, ya ce za a ci gaba da zanga-zangar a wurare daban-daban har sai gwamnatin Tarayya ta warware matsalar da ke tsakanin malaman.
Ya kara da cewa “Wannan yajin aikin da aka dade a na yi, lamarin na so yagagari kundila, kuma lamari ne da daliban ba za su dauka ba.”
A WANI LABARIN KUMA: Jiga-Jigan APC Da Tarin Magoya Bayansu, Sun Sauya Sheka Zuwa Jam’iyar PDP A Bayelsa
A yammacin jiya Litinin ne Gwamnan Douye Diri da sauran masu ruwa da tsaki na PDP su ka yi maraba da shigar wasu jiga-jigan Jam’iyar APC da tarin magoya bayan su jam’iiyar PDP a fadar gwamnatin jihar dake Yenagoa.
Gwamnan Bayelsa ya bayyana komawar mambobin a matsayin abin da ya dace idan aka yi la’akari da dadewar da suka yi da jam’iyyar kafin su tafi.