A yammacin jiya Litinin ne Gwamnan Douye Diri da sauran masu ruwa da tsaki na PDP su ka yi maraba da shigar wasu jiga-jigan Jam’iyar APC da tarin magoya bayan su jam’iiyar PDP a fadar gwamnatin jihar dake Yenagoa.
Daily Post ta ruwaito cewa, Gwamnan Bayelsa ya bayyana komawar mambobin a matsayin abin da ya dace idan aka yi la’akari da dadewar da suka yi da jam’iyyar kafin su tafi.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Tsige Shugaban Karamar Hukumar Langtang ta Arewa Dake Jihar Filato
Gwamna Diri ya kuma bayyana wadanda suka dawo a matsayin mutane masu kimar tare da nuna kwarin guiwar da za su bayar, da gudumawa mai kyau ga ci gaban jam’iyyar a jihar.
Ya yi nuni da cewa, sannu a hankali jam’iyyar PDP a Bayelsa tana komawa kan lokacin da nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben fidda gwanin jam’iyyar, wanda ya yi daidai da nasara a babban zaben dake tafe, don haka ya bukaci ‘yan jam’iyyar da su dage damtse.
Shugaban riko na jihar ya yi kira ga wadanda suka rage a jam’iyyar adawa da su sake komawa PDP, yana mai cewa jam’iyyar ta yi dai dai da dukkanin ‘yan siyasa a jihar kuma har yanzu tana da girma da za ta iya daukar masu muradin dawowa.
Tun da farko, Farfesa Seiyefa Brisibe ya ce komawa PDP tamkar dawowa gida ne, kuma yana jinsa kamar bako lokacin da yake APC.
Ya kuma yabawa Gwamna Diri bisa tsarin shugabancinsa na bai daya, wanda kuma ya sanya maslahar jihar gaba da barin duk wani abu na kashin kai ko na bangaranci.
A WANI LABARIN KUMA: Yadda Wasu A Ma’aikatar Kudi Ta Bauchi Suka Rabe Kudin Wani Mamaci N332,000 A Tsakaninsu
Wasu ma’aikatan ma’aikatar kudi ta jihar Bauchi, Nasiru Samaila da Auwal Jibrin, sun hada baki da wasu mutane biyu wajen zambar kudi naira 332,000 ga abokin aikinsu, Jibrin Adamu wanda ya rasu a watan Disambar bara.
Sun samu nasarar wannan kwamachalar ne da taimakon wani ma’aikacin gidan yanar gizo, Tijjani Mohammad da Faruq Mohammad Nasiru, dalibin Abubakar Tatari Polytechnic (ATAP) da ke ma’aikatar don samu hora na musamman