Jami’an rundunar ‘yan sanda reshen jihar Delta sun samu nasarar kwato bindiga kirar AK 47, harsashi guda goma sha biyu (12) mai girman millimita 9 da kuma harsashi guda ashirin da uku (23) da aka boye a cikin wata bakar jakar Leda
Daily Post ta ruwaito cewa, An gano kayayyakin ne a boye a karkashin kujerar fasinja na baya na Keke Napep a kasuwar Hausa dake Asaba.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Tsige Shugaban Karamar Hukumar Langtang ta Arewa Dake Jihar Filato
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe.
Ya ce an kwato kayayyakin ne a lokacin da suka yi bincike mai zurfi a kan babur din bayan wani kiran gaggawa da mazauna yankin suka yi.
A WANI LABARIN KUMA: Jiga-Jigan APC Da Tarin Magoya Bayansu, Sun Sauya Sheka Zuwa Jam’iyar PDP A Bayelsa
A yammacin jiya Litinin ne Gwamnan Douye Diri da sauran masu ruwa da tsaki na PDP su ka yi maraba da shigar wasu jiga-jigan Jam’iyar APC da tarin magoya bayan su jam’iiyar PDP a fadar gwamnatin jihar dake Yenagoa.
Gwamnan Bayelsa ya bayyana komawar mambobin a matsayin abin da ya dace idan aka yi la’akari da dadewar da suka yi da jam’iyyar kafin su tafi.