Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun tsaurara matakan tsaro a kusa da Unity Fountain da ke Abuja, inda ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar da ma’aikata a karkashin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC suka shirya a fadin kasar nan.
Ma’aikatan na jihohi 36 na tarayyar Najeriya, sun fara zanga-zangar ne a ranar Talata, inda suka gargadi gwamnatin tarayya da ta yi watsi da kiran da suka yi na bude jami’o’in Najeriya, ta hanyar biyan bukatun kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato (ASUU) da sauran kungiyoyi uku.
Manema labarai, wadanda suka isa Unity Fountain da misalin karfe 7:15 na safiyar Laraba, sun lura cewa jami’an ‘yan sandan Najeriya na jimge a wurin taron da alama don dakile duk wani alamu na sabawa doka da oda.
Daya daga cikin jami’an da ya zanta da Jaridar Daily trust, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun ranar Talata wasu takwarorinsa suka je wurin taron domin tsara dabaru da kuma dakile duk wani harin da za a iya kai wa, inda ya ce ba wai kawai an tura su domin zanga-zangar ba ne.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, jami’an ‘yan sandan na tare da takwarorinsu na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da na civil defence wato (NSCDC).
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Sojojin Najeriya Ta Sake Ceto Wasu ‘Yan Matan Makarantar Chibok 2
Idan ba a manta ba, a ranar Talata ne shugabannin kungiyar ta NLC ta kasa ta bayar da umarni ga kungiyoyin kwadago sama da 50 da su hada hannu da ‘ya’yan kungiyar domin shiga zanga-zangar a babban birnin kasar Tarayya Abuja da sauran jihohin kasar nan.
Duk da hakan, Tattakin wadda shugaban NLC, Ayuba Wabba ke jagoranta, ta shiga rana ta biyu a yau laraba kamar yadfa kungiyar kwadagon ta shirya.
A wani labarin kuma na daban.
Rahotanni sun bayyana cewa, dakarun Brigade ta 21 masu sulke sun ceto wasu ‘yan matan makarantar Chibok biyu da aka sace a jihar Borno.
Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, ya bayyana cewa sojojin sun gano ‘yan matan biyu da aka bayyana sunayensu da Hannatu Musa da Kauna Luka a karamar hukumar Bama a ranar 26 ga watan Yuli, shekaru takwas bayan sace su a ranar 14 ga watan Afrilu shekarar 2014.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa ‘yan matan sun tsere ne daga sansanin Gazuwa, hedikwatar kungiyar Jama’atu Ahlus Sunna ta lid-Da’awah wa’l-Jihad ta Boko Haram, wadda ake kira Mantari da Mallum Gabchari, da ke da tazarar kusan kilomita 9 zuwa garin Bama.
Kubucewar ‘yan matan na iya rasa nasaba da ci gaba da kai hare-haren da sojojin Operation Hadin Kai suka yi wanda ya haifar da yunwa da kaura a yankunan ‘yan ta’addar.
Rahotanni sun ce sojojin da ke garin Bama ne suka bayyana sunayen ‘yan matan biyu wadanda kuma za su tabbatar da lafiyarsu kafin su sake haduwa da iyalansu.
Idan ba a manta ba a makonnin da suka gabata sojojin sun ceto ‘yan matan Chibok biyu: Mary Dauda da Hauwa Joseph bayan sun tsere daga sansanin.