Bashir, daya daga cikin ‘ya’yan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Litinin, ya bayyana kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato ASUU a matsayin “kungiyar da ba ta da amfani”, inda ya cigaba da cewa ya kamata a wargazata a maye gurbinsu da malamai masu kula da damuwar dalibai.
Punch ta ruwaito cewa, Hakan na zuwa ne bayan ASUU ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin da take yi.
Bashir ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce, “ASUU kungiya ce mara amfani sosai, ya kamata a kawar da su a maye gurbinsu da malaman da a zahiri suke kula da dalibai.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana Cigaba Da Gwabza Kazamin Fada Tsakanin Yan tawayen Tigray Da Dakarun Habasha
Ya kara da cewa, ” Lamarin na da wata makoma ta daban ga kasar nan.”
Idan ba a manta ba, ASUU ta fara yajin aikin ne tun a ranar 14 ga Fabrairu, 2022.
A WANI LABARIN KUMA: Rikicin PDP: Wani Abu Zai Faru Nan Bada Dadewa, Inji Wike
Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, a ranar Litinin din nan, ya yi tsokaci game da rikici a cikin jam’iyyar PDP, inda ya ce har yanzu babu abin da ya faru face “wani abu zai faru” nan ba da dadewa ba.
A cewar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, babu wanda zai iya yi masa barazana domin zai yi abin da ya dace ko da kuwa ‘yan daba’ ko zagon kasa.