Auwal Rafsanjani, shugaban kungiyar sa ido kan harkokin canji (TMG), ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta gurfanar da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da tsohon ministan harkokin Neja Delta Godswill Akpabio bisa zargin karya dokar zabe.
Rafsanjani ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake magana daga Landan a shirin karin kumallo na gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis wanda wakilinmu ya sawa ido.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: Majalisar Dokokin Neja Ta Tsige Shugaban Masu Rinjaye Da Mataimakinsa
Ya ce su biyun sun karya dokar zabe ta hanyar tsayawa mukamai biyu a lokaci guda.
Sashe na 115 (D) na dokar zabe, 2022 ya nuna cewa babu wani mutum da zai sa hannu, ko ya samun fom fiye da daya a matsayin dan takarar zabe daban-daban.
Mutanen biyu za su iya zama gidan yari na tsawon shekaru biyu idan aka same su da laifi.
Akpabio da Lawan dukkansu ’yan takarar shugaban kasa ne a dandalin jam’iyyar APC a zaben 2023 wadanda Ahmed Bola Tinubu ya kayar dasu.
Sun yi ta kokarin neman tikitin takarar sanatan jam’iyyar na mazabar Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.
Sai dai Bashir Machina (Yobe ta Arewa) da Udom Ekpoudom (Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma) wadanda tun da farko suka fito a matsayin ‘yan takara a zaben fidda gwani da jami’an INEC ke kula da su a shiyyarsu ta Sanatoci, sun ki janyewa daga takarar domin share fagen mutanen biyu.
Duk da cewa APC ta mika sunayen Akpabio da Lawan ga INEC, alkalan zaben sun yi watsi da sunayen, inda suka dage cewa za ta amince da wadanda suka ci zaben fidda gwani ne kawai.
Sai dai Rafsanjani yana zargin cewa hukumar ta INEC ta ja da baya, kuma a yanzu tana kalubalantar matsayinta a kotu.
Mai fafutukar siyasar ya ce, “Ba za mu zauna muna kallon wadanda suka fafata a zaben shugaban kasa da suka sha kaye don dora kansu a kanmu ba.
“APC ba za ta iya dora mutane a kanmu ba. Dokar zabe ba ta ado ce kawai ba, ya kamata a yi biyayya. Ya kamata INEC ta tuhumi Akpabio da Lawan bisa karya doka.”
Ya yi nuni da cewa jam’iyya mai mulki na fatan biyan wadanda suka yi rashin nasara a zaben 2023 tuni ke barazana ga nasarar babban zaben 2023.
Rafsanjani ya yi kira ga INEC da ta nisanta kanta daga siyasa, ta kuma kasance mai cin gashin kanta da gaske.
A wani labarin kuma, Wata Ƴar Ƙaramar Yarinya Data Shafe Watanni 3, Ta Mutu Bayan Kwanaki 5 Da Sakin Ta
Yaro da aka saki bayan watanni uku a tsare ya mutu bayan kwana biyar
Wata ƙaramar yarinya mai suna Ewhalshoh Mandela Mairabo, wadda aka yi garkuwa da ita tare da mahaifiyarta da wasu 29, ta rasu kwanaki biyar bayan an sako ta.