Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a ranar Alhamis ya dage cewa dole Iyorchia Ayu ya sauka daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar PDP.
Wike ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shaida masa da kansa lokacin da ya lashe zaben fidda gwani a watan Mayu cewa dole Ayu ya bar mukaminsa na shugaban jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yakamata INEC Ta Tuhumi Lawan, Akpabio Da Laifin Karya Dokar Zabe – Rafsanjani
Channels TV ta ruwiaito cewa, Gwamnan ya ce murabus din Walid Jibril a matsayin shugaban kwamitin amintattu ba zai dakatar da bukatarsa na tsige Ayu ba.
A cewar Wike, batun da ke gabansa shi ne na adalci da gaskiya, yana mai cewa kasancewar ta samar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, bai kamata arewa ma ta rike shugabancin jam’iyyar ba.
“Wannan yakin za mu yi yaki da shi har zuwa karshe,” in ji gwamnan lokacin da ya kaddamar da sansanin Ahoada na Jami’ar Jihar Ribas a karamar hukumar Ahoada ta Gabas a jihar a ranar Alhamis.
Wike ya kasance a wajen taron tare da abokin sa, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
A WANI LABARIN KUMA: Da Dumi-dumi: Majalisar Dokokin Neja Ta Tsige Shugaban Masu Rinjaye Da Mataimakinsa.
Yan majalisar dokokin jihar Neja sun tsige shugaban masu rinjaye, mataimakin shugaban masu rinjaye da kuma bulaliyar majalissar dokokin jihar.
‘Yan majalisar kuma sun zabi wadanda za su gaje su nan take.