A dai dai lokacin da ake cigaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine, Sojojin Ukraine 250 dake tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dake aiki a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sun koma gida don taimakawa kasar su wajen yakar sojojin Rasha.
BBC ta ruwaito cewa, A lokacin da aka sanar da janyewar sashen kula da zirga-zirgar jiragen sama na Ukraine a watan Maris, jami’an diflomasiyya sun yi gargadin cewa lamarin zai bar tawagar Majalisar Dinkin Duniya da karancin jirage masu saukar ungulu.
KARANTA WANNAN LABARIN: A halin yanzu ana ci gaba da jana’izar Sarauniya Elizabeth ta biyu
Wadannan na da zai shafi yakin da ake yi da kungiyoyin ‘yan tawaye daban-daban da ke da sansani a cikin dazuzzukan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.
Jiragen sama masu saukar ungulu na Ukraine guda takwas sun kasance kusan kashi daya bisa uku na rundunar Majalisar Dinkin Duniya.
Rahotanni sun nuna cewa tun bayan fara mamayar Rasha a Ukraine a watan Fabrairu, Ukraine ta riga ta janye sojojinta daga sauran tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya inda ta mayar da su gida.
Da yake jawabi Jacques Ndjoli, wanda ke aiki a kwamitin tsaro na majalisar dokokin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa janyewar na da matukar muhimmanci, sai dai ya yi nuni da cewa samar da zaman lafiya a kasar alhakin sojojin Kongo ne.
Yayin da Sojojin Ukraine suka fice daga Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, kwamandan rundunar Majalisar Dinkin Duniya na Brazil, Janar Marcos da Costa, ya ce gudunmawar da sojojin suka bayar na tsawon shekaru 10 abin a yaba ne sosai.
A bangare guda kuma tawagar Jami’an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo watau Monusco na fuskantar matsin lamba a kasar.
Ana sukar MONUSCO da rashin yin wani abin da ya dace wajen maido da zaman lafiya a gabaashin kasar inda kungiyoyi da dama da ke dauke da makamai, yayin da suka kwashe shekaru 30 suna kai hare-hare, kashe mutane, yiwa mata fyade tare da wawashe albarkatun da ma’adanan dake jibge a yankin da suka haka da zinari da kuma lu’u-lu’u.
A watan Yuli daya gabata mutane 36 da suka hada da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya hudu ne suka mutu a lokacin da masu zanga-zangar suka kaiwa gine-ginen Majalisar Dinkin Duniya hari a garuruwan da ke gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Kazalika aikin wanzar da zaman lafiya a Kongo yana daya daga cikin mafi girma ayyukan wanzar da zaman lafiya 12 da Majalisar Dinkin Duniyan ta ce ta sa a gaba.
A WNAI LABARIN KUMA: Kotu Ta Kori Karar Da PDP Ta Shigar Kan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Na APC Da LP
Mai shari’a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin din nan ya yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar na neman a soke takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu da na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi bisa zargin sauya sheka ba bisa ka’ida ba abokan tafiyarsu.
Alkalin ya ce PDP tana da nufin tada hankalin abokan hamayya a zaben shugaban kasa na 2023.