Rundunar yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da cewa, wasu yan bindiga da ba’asan ko suwaye ba, sun kai wa motar kudi hari a yankin garin Ore dake jihar.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar yan sandan ta kuma tabbatar da kashe direban motar da jami’in ta guda a yayin harin.
Kamfanin dillancin labarai NAN ya bayyana cewa, an Kai harin ne a yammacin jiya Laraba a garin Ore, dake ƙaramar hukumar Odigbo na jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban jam’iyar PDP na Legas ya rasu
Kazalika majiyar jaridar Dimokuradiyya ta bayyana cewa, wannan harin na zuwa ne kimanin makonni biyu bayan harin da aka kai wa motar kudi a garin Emure-Ile dake jihar ta Ondo.
Wani shaidan gani da ido da ya bukaci asakaye sunan shi ya ce, “Ƴan fashin sun bude wa motar kudin wuta ne, yayin da take tafiya Kuma ta ke dauke da adadin kudi da ba a bayyana iyakarssu ba, tare da motar yan sanda dake ba motar kudin tsaro” inji shi.
“An kashe direban motar da jami’in dan sanda guda yayin harin, sannan an sace wani adadin kudi” a cewar shi.
A na ta bangaren,Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da afkuwar lamarin inda tta ce, yan sanda suna kan neman maharan.
A wani labarin Kuma na daban
Akalla mutane 8 suka mutu, sakamakon wani hari da aka kai a garin Yelewta dake karamar hukumar Guma na jihar Benue.
Sai dun gani da Ido sun bayyana cewa, an Kai harin ne yayin da yan kasuwa ke kokarin rufe shagunan su.
Shugaban karamar hukumar Guma Caleb Aba ya bayyana wa manema labarai ta wayar salula a garin Makurdi cewa, an kashe mutane a harin.
Aba ya ce, an kai harin ne a kasuwar Yelewta, inda suka kashe mutane 8, lokacin da yan kasuwa ke kokarin rufe shagunan su.
Shugaban karamar hukumar ya kuma ce, tuni aka kai wadanda suka sami raunika asibiti, domin duba lafiyar su.
Anata bangaren jami’ar hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar DSP Catherine Anene ta tabbatar da harin, Amma ta ce, mutane 6 ne yan bindigan suka kashe sanadiyar harin.
Ta kara da cewa, “Jiya 24 ga watan Agustan shekarar 2021, da musalin karfe 7:45 na yammaci, rundunar yan sanda ta sami bayanan cewa, wasu yan bindiga da ba’asan ko suwaye ba, sun afka yankin Yelwata, inda suka kaiwa wani yanki da ke kusa daji hari.” Inji ta.
Comments 1