Rahotanni na nuna cewa, Kimanin sojoji 11 sun rasa rayukansu yayin wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wani sansanin sojojin a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Daruruwan ‘yan bindigan sun isa sansanin ne a kusa da kauyen Polwire a daran jiya Litinin kuma sun dauki wani lokaci suna musayar wuta da sojojin da ke cikin barikin.
Wata majiya daga rundunar sojin ta kasa, ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun isa sansanin ne bisa babura dauke da manyan makamai, ciki har da bindiga mai harba gurnati.
Majiyar ta ce an shafe sa’a biyu ana gwabzawa kazamin fada tsakanin bangarorin biyu, kafin ‘yan bindigan suka iya kore sojojin daga cikin sansanin.
Sai dai harkawo hada wannan rahoton shelkwatar rundunar soji ta kasa Bata fitar da wani sanarwa kan lamarin ba.