Yan bindiga sun kashe akalla Mutane 36 yayin da wasu da dama suka sami raunika, a wani sabon hari da ka Kai a gundumar Ahwol, na yanki Naraguta dake karamar hukumar Jos ta Arewa dake jihar Fulato
Rahotanni sun nuna cewa, Maharan sun afka yankin ne dauke da muggan makamai da musalin karfe goma na daran jiya Talata .inda suka kashe mutane da dama, tare da jikkata wasu da aka kai asibitin horaswa na jami’ar Jos, dake babban birnin jihar.
Babban basaraken a jihar Ujah Johnson Jauro ya tabbatar da afkuwar lamarin ga manema labarai a yau Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibar Jami’ar Kwara
A cewar basaraken, ” Eh tabbas na Sami labarin yan bindiga sun afka yankin Naraguta, inda suka kashe mutane da kuma jikakkata wasu da daba, Amma haryanzu muna ci gaba da gudanar da bincike” inji shi.
Kazalika kansilar mazabar Ahwol Yusuf Ali Shima ya tabbatar da kai harin, inda ya ce, Maharan sun kone mutane da yarukan su yayain kai harin
Har’ila yau wani mazaunin garin Mai suna Jeremiah Bulus ya ce, ” an Kai wasu gawar-wakin asibiti, ya yin da haryanzu mutane suke dada zakulo gawar-wakin mutane a cikin gidaje, sabida sanyawa gidaje wuta da maharan suka yi, ya yin harin,” inji shi.
A cewar Kansilan, yan bindigar sun fara lalata gadar karfe da ke haɗa yankin da wasu yankuna, kafin su kai hari kan mutanen, wanda hakan ya yi wa jami’an tsaro wuya su kai dauki yankin, lokacin da aka tuntube su kan hare -haren.
Comments 1