Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kashe sama da wasu mutane matafiya 9, ciki har da jarirai, a kauyen Zankoro da ke kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, a ranar Lahadi.
Haka zalika, akalla mutane 11 ne aka yi garkuwa da su a wannan ranar a kauyen Dan Kungi da ke karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga shugaban kungiyar ci gaban Birnin Gwari, Mr Salisu Haruna, a ranar Litinin, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
KARANTA WANNAN: Babbar magana: Kwamishina a Anambra ya yi murabus
Sanarwar mai taken, ‘Yawaitar yan bindiga da kashe kashe a Birnin Gwari,’ ta kara da cewa sama da mutane 40 ne aka sace su a tsakanin ranar 20 ga watan Disamba 2020 zuwa ranar 4 ga watan Janairu 2021, inda wasu da aka yi garkuwa da su ke fama da matsanancin rashin lafiya.
Kungiyar BEPU, ta yi kira ga gwamnati da ta kawo jami’an agajin gaggawa domin daƙile hare haren yan bindiga da masu garkuwa da mutane a hanyar Birnin Gwari, Kaduna da kuma hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua.
Sai dai duk wani kokari na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ƴan sanda na jihar, Mohammed Jalige ya ci tura, inda ba ya daukar waya kuma bai maido da amsar sakon kar ta kwana ba.