Akalla Mutum 14 ne suka mutu, a wani sabon hari da yan bindiga su ka kai kauyen Mado dake yankin Mabushi a Masarautar Atyap na karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Harin da aka kai a daran jiya Asabar, ya shafi wasu gidaje da dama.
Lokacin da ya ke zanta wa da manema labarai Shugaban kwamitin jami’an Sakai na Masarautar Atyap ACPSPC Mr John Bala Gora, ya bayyana damuwarsa dangane da harin, duk da yunkurin da wo da zaman lafiya a yankin.
Kazalika ya kuma kara yin kira ga sauran jami’an tsaro, da su kara zage damtse wajan tsare “al’umar masarautar masu son zaman lafiya.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Daliban Makarantar Baptist 15 sun shaki iskar yanci
Kazalika awani makamancin wannan kuma, wani rugar Fulani dake yankin Kankada a gundumar Madakiya dake Masarautar Bajju duk dai a karamar hukumar Zangon Kataf din na jihar Kaduna, yan bindigan sun farmaki Rugan, inda suka kone shi baki daya a safiyar yau lahadi.
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewar, wata mata mazauniyar Rugar Fulani Mai suna Halima Haruna, bayan ta tsira daga harin kuma ta sami mafakan a wani Caji ofis din yan sanda dake Zonkwa ta ce, Maharan sun farmake sune da sanyin safiyar yau lahadi.
Halima wacce matar Ardo na Kankada ce, ta kara da cewa, ta ga gawar mace da na Miji, lokacin da take kokarin nemar mafaka.
“An matsamana yin gudu domin neman wurin buya, ya yin da wasu mutane daga cikin mu, suka fantsama cikin daji.” Inji ta.
” Bansan me ya faru da su ba a yanzu. Amma munyi gudun akalla awa uku, kafin isowar jami’an tsaro da suka debemu zuwa caji ofis din Zonkwa. Kuma an kone dukkannin gidajen mu” a cewar Halima.
Kazalika ta ci gaba da cewa, Yan bindigan sun ce, sun zo daukar fansa ne, kan abun da a kai musu, a wani yanki dake kusa da Samarun Kataf “Wanda bamusan komai ba kan hakan” inji ta.
Comments 1