By Abbas Yakubu Yaura
A jiya ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Gada dake karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara, tare da kashe basaraken al’ummar yankin Umaru Bawan-Allah tare da wasu mazauna garin uku a cikin lamarin.
Sakataren Masarautar Bungudu, Usman Ahmad, ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 1:00 na dare inda suka yi ta tayar da kayar baya ayankin.
Malam Ahmad ya ce majalisar masarautar ta sanar da karfe 4:00 na yammacin jiya domin jana’izar sarkin gargajiya da sauran wadanda aka kashe.
Al’ummar Gada na da tazarar kilomita bakwai daga Bungudu, hedikwatar karamar hukumar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Lamarin ya faru ne bayan watanni uku da sace Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru, a hanyar Kaduna zuwa Abuja a watan Satumba. Ya kwashe kwanaki 32 a tsare kafin a sake shi.
Ana dai kallon Sarkin Bungundu a matsayin wanda ya fi sarkin gargajiya na Gada wanda aka kashe a harin na jiya.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun shafe kusan sa’o’i hudu suna gudanar da ayyukansu, inda suka yi ta kashe-kashe da nakasa mutane da kuma yi wa mata fyade yadda suka ga dama.
Sun ce ‘yan bindigar sun kona kayan abinci da motocin da aka ajiye a fadar sarkin gargajiyar.
Sai dai duk kokarin tuntubar mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu, ba’a sameshi ba a lokacin da wakilinmu ya tuntube shi a jiya da safe a kokarinsa na jin martanin ‘yan sanda kan lamarin.
Hare-haren da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke kaiwa al’umma a Zamfara ya zama ruwan dare inda aka kashe daruruwan mutane ko kuma sace su a shekarar 2021. Baya ga Zamfara, sauran jihohin Arewa maso Yamma da ke fuskantar irin wadannan hare-hare sun hada da Sokoto, Katsina da Kaduna.
Ana ci gaba da kai hare-hare duk da yawan jami’an tsaro da aka tura yankin.
A ranar Talata ne gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya shawarci al’ummar jihar da su kasance masu rike da makamai domin kare kansu daga ‘yan bindigar.