Biyo bayan wani samame da wasu ‘yan bindiga suka kai a kauyen Kidandan dake karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, mazauna yankin sun kaurace wa gidajen kakanninsu.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun shafe sa’o’i da dama suna harbe-harbe, inda suka kashe wasu daga cikin al’ummar yankin kafin su yi awon gaba da wasu daga cikinsu.
Karanta nanKa rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa ga hidimomin mulki – Ƴan Ƙasa Ga Tinubu
A cewar wata majiya, ‘yan bindigar sun fusata ne a lokacin da manoman suka kasa biyan harajin da aka dora musu tun da farko.
Harin na Kidandan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wani harin bam da wata mota mara matuki ta Sojoji ta kai a kauyen Tudun Biri dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
A wani labarin kumaDa Dumi-Dumi: CBN Ya Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Yadda Ake Yada Jabun Kudaden Naira
Majiyar ta shaidawa DAILY POST cewa: kwanaki shida da suka gabata ‘yan fashi suna zuwa garin Kidandan suzo su firgita mu, suka yi awon gaba da mutanenmu. Kowane mazaunin garin Kidandan yana rayuwa cikin tsananin tsoro.
Ya kuma bayyana cewa mata da kananan yara ta rasa ranta a lokacin da take neman tsira, inda ya ce da yawa daga cikin wadanda suka yi hijirar na tafiya ne domin tsira.