Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu fastoci uku a kan hanyar Ochadamu-Okele-Ejule a ranar Juma’a a karamar hukumar Ofu ta jihar, sun bukaci a biya su naira Milliyan 80 a matsayin kudin fansa.
Daily trust ta ruwaito cewa daya daga cikin wadanda da aka sace akwia Fasto Sunday Emmanuel Abbah daga karamar hukumar Olamaboro, Wanda yake zaune a Lokoja.
Fastocin uku an ce suna kan hanyarsu ne daga Lokoja domin yin hidima, hahin da ‘yan ta’adda a wata Suka farmake su a Wani yanki dake gabashin Jihar Kogi a lokacin da maharan suka tare motarsu a kusa da yankin Ochadamu zwa Okele-Ejule
Wata majiya daga daya daga cikin fastocin da aka sace ta ce masu garkuwar sun yi kira waya inda suka bukaci da a biya su Naira Milliyan 80 kafin a sako fastocin.
Sai dai rundunar Yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin na garkuwa da mutane, inda ta ce ta tura jami’anta zuwa domin ganin an sako mutanen.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar Yan sandan jihar, SP William Aya, “Rundunar ta na sane kuma tana kokarin ganin an sake su”.