By Ishaq Dabai
Masu garkuwa da mutane sun sake sakin wasu dalibai 10 na makarantar Baptist dake Kaduna bayan sun shafe kwanaki 81 a hannun masu garkuwa da mutane.
Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya CAN reshen jihar Kaduna, Rabaran Joseph Hayab,shine wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yammacin Lahadi.Hayab, wanda ya tabbatar da cewa 11 daga cikin daliban har yanzu suna rike a Hannun ‘yan bindigar, inda ya bayyana fatan suma za a sake su nan ba da jimawa ba.
“Muna gode wa dukkan‘ ‘yan Najeriya saboda addu’o’insu da goyon bayansu. Kuma muna dogara ga Allah cewa sauran ma za a sake su nan ba da jimawa ba, ”in ji shi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ‘yan bindigar tun a ranar 5 ga watan Yuli ne inda suka shiga makarantar Baptist dake Damishi a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia, karamar hukumar Chikun inda suka yi awon gaba da dalibai 121.
Tun daga lokacin ‘yan bindigar suke sakin ɗalibai kadan kadan bayan an karɓi fansa a miliyoyin.