Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun Hallaka jami’an yan sanda hudu da soji biyu a wani shingen ababen hawa a titin Owerri zuwa Fatakwal na karamar hukumar Ikwere dake Jihar Ribas.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya auku ne tun a daren jiya asabar amma labarin bai buya gari ba sai a sanyin safiyar yau Lahadi.
Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani dangane da adadin yan bindigar da aka kashe.
A yan baya-bayan nan dai lamuran tsaro na ci gaba da ta’azzara a yankin Kudancin Kasar nan, batun da aka alakantawa da ya’yan kungiyar Inyamurai ta IPOB.