By Ishaq Dabai
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan Bindiga sunyi garkuwa da Sarkin Wawa, Dakta Muhmud Ahmed Aliyu a fadarsa dake karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.
Rahotannin sun bayyana cewa anyi garkuwa da Sarkin gargajiyar da misalin karfe 10 na daren ranar asabar.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun sa sarkin a tsakiya tare da harbi akan iska kuma suna sanye da kayan sarki irin na sojoji suka tafi dashi ta tashar kainji.
Sannan yace ya fahimci yan fashin suna da hadari inda suka futa a babura sannan kafin sutafi saida suka harbi mutane biyu a wajen.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sanda na jihar Abiodum Wasiu ya tabbatar da faruwar hadarin a zantawar sa da manema labarai.
Abiodun yace yanzu haka sunbi bayan ‘yan bindigar dan kubutar da Dagacin.
Sannan yayi kira ga mazauna yankin da su baiwa jami’an tsaro goyan baya wajen basu nayan sirri dan yaki da masu garkuwa da yan bindiga.