Yan fansho a jihar Taraba sun fito kan titunan babban birnin jihar wato Jalingo, domin nuna rashin amincewarsu da rashin biyansu kudaden fansho da alawus-alawus da gwamnatin jihar ta yi.
‘Yan fanshon da suka kasance daga kananan hukumomi 16 na jihar, sun yi barazanar kauracewa zaben 2023 matukar ba a biya su hakkokinsu na sama da shekaru takwas da suka haura Naira biliyan 30 ba.
‘Yan fanshon da suka haura sama da dari ne suka mamaye gidan gwamnati dauke da kwalaye da rubuce-rubuce daban-daban kamar su ‘Mun gaji da karya da alkawuran karya’ da ‘Ishaku ya biya mu kudinmu’ daga nan suka wuce zuwa majalisar dokokin jihar.
A gidan gwamnati dai jami’an tsaron da ke bakin aikinsu sun hana su shiga a yayin da masu zanga-zangar ke ci gaba da tofin Alla tsine kan gwamnati da jami’anta.
Daga baya an ba shugaban kungiyar ‘yan fansho na jiha da sakataren kungiyar ‘yan fansho izinin shiga su mika wasikar su ga gwamnan a ofishin rejista na fadar gwamnati saboda rashin halartar manyan jami’an gwamnati da za su halarta.
Daga gidan gwamnati sun zarce zuwa majalisar dokokin jihar inda kuma suka gabatar da wasika ga shugaban majalisar duk da cewa shugaban majalisar da sauran mambobin majalisar ba su samu damar yi musu jawabi ba.
Shugaban kungiyar ‘yan fansho ta kasa (NUP) reshen jihar, Kwamared Kefas Katan wanda ya jagoranci zanga-zangar, ya shaida wa manema labarai cewa sun gudanar da zanga-zangar ne saboda rashin kulawa da gwamnati ta yi kan halin da suke ciki.
Da yake lissafo bukatunsu daga gwamnati, Katan ya bayyana cewa, “Sakamakon da muka samu ya biyo bayan aiwatar da mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati a shekarar 2019 da kuma karin kashi 33 cikin 100 na fensho da aka amince da su tun 2014 kuma har yanzu ba a biya fensho da garatuti.
Shugaban ya koka da yadda ’yan fansho a jihar ke mutuwa shiru saboda an kori da yawa daga cikin gidajen da suka yi hayar ko kuma an cire ’ya’yansu daga makarantu yayin da wasu da dama kuma suka mutu saboda rashin samun magunguna.
Sai dai ya jaddada cewa ba za su ji tsoro ba ko kuma su ci gaba da neman ‘yancinsu har sai an ba su hakkinsu yana mai cewa duk ‘yan fansho da ke fadin jihar za a tattaro su su mamaye gidajen gwamnati da majalisar dokoki da sauran muhimman wurare idan gwamnati ta gaza. don halartar su, ya kara da cewa za su ci gaba da kasancewa a can har sai an biya su hakkokinsu.